[8/7, 3:28 PM] Afreen ce: ~SAFNA TA~
B¥
{Faty afreen}
*👑Queens Online writers*
*(Q.O.W)👑*
_(Home for wisdom & excellent writers)_
Bismillahir-rahmanir-rahim..
*01*
"Abdulrahman kana sane cewar bazan yarda ka
aure safnaba ko?"
"haba umma me safna ta miki naga dai dikwani
so da gataba wanda ba kyawa safna"
afusace mumy ta kallesa tana fadin
"abdul fitarmin a daki tin kafin na bata maka rai"
"amm mu.."
be karasa zancensa ba mumy ta daka masa
tsawa ba shiri ya fita daga dakin..be zarce ko ina
ba se dakin safna..leqawa yayi ya ganta dauke
da jinjirarta daga bisani ta kwantar da ita...
Zancen zuci ya somayi yana fadin
"karki damu safna i sha Allah nayi alkawarin zan
sharemiki hawayen ki keda miemie bazan taba
bari ku wulakanta ba..."
yana kaiwa nan ya shiga cikin dakin yayi yana
murmushi ya dauki miemie wasa ya soma mata
dakagansa kasan yana cikin farinciki..
Safna kuwa da mamaki take kallonsa ita ma
zancan zuci ta somayi tana fadin
"gsky yaya abdul ya canja..daga randa na haifi
miemie yake nuna mana so da kulawa.... jibi
ranar suna shiya siya ragon suna.ga uban kayan
daya mana... amma ada ba wanda ya abdul ya
tsana a gidanan kamar ni..insha Allah bazan taba
yafewa wanda ya mun wanan abu ba.ya ci mun
mutunci yasa na zama abar qyama da nuni.."
tana kaiwa nan tafashe da kuka... abdulrahman
kuwa na jin hk da gudu yayo kanta yana tmbyrta
abinda ya sameta...
*washe gari*
kwance abdulrahman yake yasa hanunsa saman
kai idonsa narufe yana tinani
"kiyi hkr safna nasan na bata miki rayuwa na
cuceki kiyafemin..kuma insha Allah zan kula da
ke da miemie"
kukan miemie ne ya dawo dashi daga tunanin da
yakeyi.bashiri ya miqe da gudu ya isa dakin..
hanun mumy yaga miemie tana faman kuka
"mumy meke faruwane? "
"yauwa abdul kama safna magana kila zata fi jin
naka tin jiya daddare rabon data shayar da
miemie"
Zaro idanu yayi a tsorace kuma cike da
mamaki...gaban safna ya nufa ya soma roqonta
harda hawaye...itako jiki sanyaye ta miqe ta
karbi miemie...bin abdulrahman sukai da kallo ita
da mumy cike da mamakin irin son da abdul
yakeyiwa miemie...
ita dai mumy abibda ke bata mamaki shine tinda
take da abdulrahman be taba nunawa wani yaro
kulawa irin yanda yakewa miemie ba... tabe baki
mumy tayi ta miqe ta fita domin kawo wa safna
abinci..
*Night*
motar abdul ce ta shigo harabar gidan ya pakata
a parking lot...yayinda me gadi ke rufe gate din..
yana shiga cikin gida ya nufi dakin safna...sbd
kukan miemie dayake jiyowa..yana shiga hanunsa
dauke da ledoji guda biyu cike da kaya.
bece dasu komai ba ya hade rai ya ajiye kayan
ya sunkuci miemie ya hau rirrigata...
"haba yaza ayi ace kullun kudinga wahalar da
yarinya kuna barinta tana kuku?
fadan dayakeyi ne yasa suka sake baki suna
kallonsa....
"abdul ko kai ka haifi 'yar nan ban sani ba?"
acewar mumy ta fada tana kallonsa...shiko
kamar an tin xirasa a fusace yasoma fadin
"ehmana nina haifeta"....
atare suka hade baki suna fadin "*kaika
haifeta"* ???
aika aijkan da yaga yana neman yi ne yasa ya
bar dakin dasauri.mumy kuwa miqewa taiyi tabi
bayansa har tana tuntube..
(Afreen)
[8/7, 3:28 PM] Afreen ce: ~SAFNA TA~
B¥
{Faty Afreen}
*👑Queens Online writers*
*(Q.O.W)👑*
_(Home for wisdom & excellent writers)_
*02*
Dasauri abdul ya sige dakinsa mumy ta turo qofa
"me kace abdulrahman"
wayincewa yayi kamar besan me take nufi ba..
"me nace fa mumy?"
"zaka mayar dani shasha sha ne? kace kai ka
haifi miemie"
"kaiii mumy ynxu abinda ya dameki kenan..ynxu
tinda ni nake wa miemie komai ai innace ni
mahaifinta ne bakomai ai ko?'"
mumy batace komai ba ta fice daga dakin..ajiyar
zuciyar ya sauke tare da kwanciya kan gado...
*****
"Alh. wai kai baka lura da hallaiyyar abdulrahman
ne?"
alh. dake ta aiki da laptop dinsa ya amsa batare
da ya dago ba..
"hallaiyyarsa tame fa?"
"game da miemie fa kaga irin dawainiyar da
yakeyi akanta"
mumy ta fada atakaice...
dago kai alh. yayi tare da fadin
"toh in be mata ba wa kikeso ya mata?nagadai
safna 'ya ce agurinki..kuma shima danki ne tih
dan yawa miemie shine ya zama laifi?"
gyada kai mumy tayi alamun a'ah..
canxa hirar mumy tayi ganin alh. be gano inda ta
dosa ba...dan ita kam a gasky tana son safna
amma saboda abinda ya samu safna batajin zata
yarda abdurahman ya auri safna...
*years ago*[flash back]
mumy ce cikin wata mota driver na tuqata.
wayarta ce ta soma ruri..sunan Abdulrahman ne
ya bayyana a screen din wayar daidai ta amsa
wayar kenan ji kaje qiiiiiii salati suka faryi dasauri
suka fitoh daga cikin motar
yarinya ce yar shekara 9 kwane a kasa jini na
fita ta hancinta kayan cikita har sun soma
yagewa tsabar datti data musu yawa..
dasauri mumy ta sa driver ya dauki yarityar ya
sata a mota basu tsaya ko inna base asibiti.ba
bata lokaci aka shiga dubata...
****
Zaune mumy take tana bama yarinyarnan
abinci..bayan ta kammala ne mumy ta kalleta
tana fadin
"me suanki?"
amsa ta bata da cewar sunanta balkisu..murmus
hi mumy tayi tana fadin ina ne gidanku?
nanfa balkisu ta fara kuka tana girgiza
ka..ahankali mumy ta rarrasheta kafin ta
tambayeta inda gidansu yake.nan take bata
labarin cewar sun xo xiyara ne nan garin motarsu
tayi hatsari ita kuma balkisu ganin iyayenta basa
motsi shiyasa ta baer gurin xuwa nemo
mutane...tana dawowa taga mutane dayawa
agurin..mutanen na watsewa taga ba iyayenta
agurin alamun an tafi dasu...
nan mumy ta rarrashe..bayan wasu kwanaki aka
sallamosu daga asibitin gida mumy ta wuce da
ita ..nan ta soma kiranta da safna...gata sosai
take sha agun mumy da dady..
Tarihin *mumy da daddy*
{next page}
(Afreen)
[8/7, 3:29 PM] Afreen ce: ~SAFNA TA~
B¥
{Faty afreen}
*👑Queens Online writers*
*(Q.O.W)👑*
_(Home for wisdom & excellent writers)_
*03*
Alh.Kabiru babban dan kasuwa ne..shine babba
agun mahaifinsa yanada kannai guda biyar mata
uku maza biyu...
dik a gidansu shine yasamu damar yin karatu me
zirfi..yana kammalawa yasamu aikinsa me kyau
..bayan yasamu aiki me Allah yawa mahaifiyarsa
rasuwa...
bayan shekara da samun aikinsa ya hadu da
haj.Amina (mumy)..
bayan auransu sunshafe shekaru da dama
haj.Amina bats haihuwa dan haka kannansa suka
sata agaba da gori har suna samo masa wata
matar ...acikin ikon Allah acikin shekarsu ta 6
haj.Amina tasamu ciki tahaifi yaro me suna
*Abdulrahman* babu irin gata da syyr da Abdul
besha ba agun iyayensa...harya firma ya fara
krtu Inda yana gama sec. dinsa Alh.ya bass
zabin garin da yakeson zuwa..ghana yace dan hk
ba bata lkci aka nemar masa abinda yakeso...
*******
(cigaba)
Bayan dawowar Balkisu gidan suka samata
*SAFNA* babu abinda ta nema ta rasa agidan ..
makaranta kuwa wacce ta amsa sunanta mkrnta
ta yaran masu gudu akasata..babu Wanda ya isa
ya taba safna mumy ta qyalesa bata nuna
bacinranta ba..
kanan dady kuwa ba irin zagin da mumy bata sha
agunsu ba akan safna amma dik ta qyale dan
India sabo yaci ace ta saba.. ahaka harta gama
primary dinta ..alkcin safna ta kara kyau
dakaganta kasan Yar gata ce..makarantar
secondary akasata (prince &princess) academy...
mota dady soya mata ya sama mata driver..first
day dinta at skull kuwa ansha kallo dan dik
wacce ta debo gajiyarta seta ce tanaso su zama
kawaye..itadai safna nata ido sedai murmushi
Satinta biyu a skull tana zaune itada kawarta
hameeda suna duba note din da aka basu..wata
ce taxo wucewa safna bata ankare ba se ji tayi
an takata... nanah ce class mate dinsu tare da
kawayenta hafsah da nafisa..
hameeda ce ta bude baki zatai magana safna ta
hanata dan ta lura da take taken nanah tinda
tashigo makarantar tasu bata so daya ba...
washe gari kuwa safna tayi sammakon zuwa skul
ita da hameeda ...zaune suke suna karatu har
yan class din suka fara taruwa..saboda surutu
yasa safna da hameeda suka fita waje basu fi
mnti biyar da fita ba suka ga an wurgo jakar
safna waje..
safna miqewa tayi ta nufi ajin dab ganin waye
.tana tambaya akace ai nana ce ba bata lkci ta
nufi inda take ta dauketa da mari afusace itama
nanah ta miqe ta rama..
"ni kika jefarwa jaka kuma ni kika Mara?"
acewar safna dake riqe da kuncinta
tsaki nana tayi tare da fadin "ehdin"
safna bata kuma cewa komai ba ta fice daga ajin
Inda driver dinta yake ta nufa tare da fadin ya
tashi su tafi Gida..
jikinsa Na rawa ya bude mata qofa suka wuce...
suna isa gida ta fitoh da sauri kofar Palo ta nufa
tana zuwa ta cire hijab dinta ta fashe da kuka ta
tura qofar palon...
tana shiga ta tatar dawani zaune *abdulrahman*
ne kasan cewar ita ba saninsa tayi ba ta turo
baki ra cigaba da kukanta tana kiran
mumy.shima sake baki yayi yana kallonta iya
saninsa basuda yarinya kamarta a gida...
agigice mumy ta fitoh Rana tmbyrta meya
faru...nanfa mamaki ya kara cikasa
(Afreen)
[8/7, 3:29 PM] Afreen ce: ~SAFNA TA~
B¥
{Faty afreen}
*👑Queens Online writers*
*(Q.O.W)*
_(Home for wisdom & excellent writers)_
*04*
Cikin shasheqar kuka safna ta fara magana
"mumy wata yarinya na ajiye jakata a class ta
wurga min it's wake name Na mata magana
shine ta mareni..."
"wat!!!! ta marrki?"
mumy ta fada cike da mamaki...afusace mumy
ta day mayafinta taja safna suka fits akabar
abdulrahman da sake baki..hard a Sosa idanunsa
ko mafarki take...
tinani ya faryi kardai mumy ta sake haihuwane
bats fada masa ba
.. miqewa yayi ya shige dakinsa ..
Mumy kuwa Suns is a daidai nan ana assembly...
teacher Nasir ne ya nufo Inda su mumy suke tin
kafin su karaso
gaisawa sukayi kafin ya kalli safna wacce me
kuka.. kafin ya soma fadin
"Yar autar mumy ya akayi ne?"
Lamar mumy Na jira cikin Dada ta soma masa
bayanin abinda ya faru.. tmbyrt wacece kai ta
nuna nanah.. takaice dai bulala 6 akawa nanah a
assembly tin daga ranar safna ta samu saukin ta
amma bar iyau basa magana...
mumy na komawa gida Abdul ya soma mata
tambayoyi akan safna nan ta basa lbrn
safna...amaimakon yaji tausayinta sema
haushinta da yakeji...
tin daga ranar muddin Abdul na palo safna bata
sakewa... kome takeyi idan ta gansa zata dena
ba irin xagin da Natasha agurinsa...
Akwan atashi bawuya bayan safna ta kammala
sec. skul dinta da wata biyu Abdul ya gana
krtunsa shima yadawo Nigeria inda yake aiki a
company din dady...
bayan dawowar Abdul Nigeria me ya hadu da
haneef abokinsa amma tin lkcin halayen Abdul ya
canja Kazan cewar haneef shayeshaye hakan
yasa Abdul shima ya koya...
Ranar Saturday
kwance safna take saman kafar mumy tana mata
tsifa..Abdul ya shigo yana kallon inda suke yayi
tsaki dasauri suka kalle inda yake
"zo nan damage innason magana Sakai"
acewar mumy
turo baki yayi ya nufo inda suke ya xauna a
kujera..
"gani mum"
"Abdul inna kaje jiya we large biyu ka dawo?"
Sosa qeya yasomayi yana inda inda..
"mumy gidansu haneef mukaje fa"
"ni zaka rainawa hankali su iyayen haneef din
basuda hankali me?"
shiru Abdul yayi be kuma cewa komai ba..
"abdul innafa ankare dakai wacce iriyar dabi'a
kadauko ta shaye shaye?"
dasauri ya daga ido ze kalli mumy sukai ido hudu
da safna...hararta yayi dasauri ta sunkuyar da
kai..
"kabani ansa kayi shiru"
mumy ta qara fada ranta a bace..
"kiyi hkr mumy"
"ka faggauta canja halayyarka idan ba hk ba toh
wlhi in fadawa dadynka..
miqewa yayi tare da bata hkr ya shige
dakinsa...yana Shiga ya saw a kofar key ya
kwanta a kan gada..
ajiyar zuciya ya saukar tare da runtse idanunsa..
"ya akai mumy ta sani?"
fuskar safna ce ya soma gani a idanunsa yadda
take kwance a kafar mumy...tsaki yayi ya miqe
ya jawo kwalbar wani drink Wanda ajiki aka rbt
alcoholic budewa yayi ya soma kwankwada
kamar an aikosa har iyau idanunsa na runtse
kyakyawar fuskar safna take kallo.. da Saddam
ta kallesa...wani irin murmushi ya saki nan da
nan yanayinsa ya kuma sauyawa a fusace ya
miqe ya nufi toilet domin watsaruwa...
washe gari Abdul na zaune shida haneef a
dakinsa..
"kaini yinwa nakeji fa"
acewar haneef..murmushi Abdul yayi tare da
tmbyrsa me zeci..indomie haneef ya fada kafin
ya miqe ya five..
Abdul Na fitowa sukai cin karo da safna juyawa
tayi data gudu da Sauri ya kamota ta..
"me kisaurareni kiji..runtse idanunta tayi..shiko
tsayawa yayi yana kallonta daga bisani ya soma
fadin
"kije kitchen ki data mana indomie ki kawo mun
dakina .."
turo baki tayi ta bata sakinta yayi ta juya Rana
tafiya tanacqunqunai murmushi yavqarayi ya juya
ya koma dakinsa...
bayan wasu mintina ahankali safna ta tuto kofar
dakin Abdul daidai Sadda yasakwalbar alcoholic
drink din abakinsa dasauri ya cire ..afusace ya
miqe ya nufota
"me ba akoya mini kwankwasa kofa ba ko?"
rawa jikinta ya farayi tana girgiza kai bakinta na
rawa ta soma basa hkr...karban plate din yayi
tare da Jan kunenta..
"saura kije kifadawa mumy abinda kika
gani..munafuka kawai"
yana saketa tayi waje da gudu tan fadin ni ba
munafuka bace..
ransa bace ya dawo ya sauna..
"kai amma yarinyarnan tayi fa..dama kana da.."
be karasa xancensa ba Abdul ya dakatar dashi..
"kai ya isa hknan me ya kai idonka wurin inna
ruwanka da kanwata?"
murmushin mugunta haneef yayi tare da cije
lebe..Abdul Na kallonsa dan haka ya bigi kafadar
haneef yana fading
"kaii don't try to do any thing stupid in ba hk ba
xanyi maganinka..kanwata ba ajinka bace..
(Afreen)
Yesterday at 10:35am · Public
Boost this post for $3 to reach up to 5,700
people.
57 People Reached
[8/7, 3:30 PM] Afreen ce: ~SAFNA TA~
B¥
{Faty afreen}
*👑Queens Online writers*
*(Q.O.W)👑*
_(Home for wisdom & Excellent writers)_
*05*
"cool down my man ba abinda zanyi kaga matso
mana da delicious din princess"
acewar haneef..harara Abdul ya watsa masa Dan
hk ya soma dariya tare da daga hanunwansa
sama..
"oh sory Wanda sis dinka ta dafa"
takaici ne ya cika Abdul be ce komai ba ta dawo
plate din abincin suka fara ci.. Abdul na kai loma
daya yadan lumshe idanunsa tare da budesu
yana murmushi aransa yana fadin "ashe dai ta
iya girki"
yana kaiwa nan ya tsinksyi murtar haneef yana
fadin .." uhmmm wow did is so delicious gsky ta
iya cook"
Abdul besan sanda yayi tsaki ba yaja plate din
yana cewa "wallahi bazakaci shi ba..muje waje
insiya mana"
hkr haneef ya soma ba Abdul amma fur yaqi
karba ahk suka fice...
*Night*
yauma kamar kullun cikin layi Abdul ya shigo
gida ahankali yana tangadi ya Shiga dakinsa
kangado ya fada yana fadin
"wallahi wallahiiiii inna santa"
"shiiii" yafada tare da bige bakinsa da sauri ya
qara fadin
"banasanta"!!!
can kuma ya qara fadin "Abdul na santa
mana..kyakyawa ce"
dariya ya fashe da ahaka yayita surutansa had
barci ya dauke shi...
*MONTH LATER*
Zaune Abdul yake a Palo yana kallo..daidai nan
safna da hameeda suka fitoh sunci kwalliya
mumy ce ta fitoh tana Waya..tana gamawa ta
kalli su safna
"Yan mata na harkun fitoh?"
dariya sukai tare da amsa mata da eh..shagwaba
safna ta farayiwa mumy nanfa Abdul ya tsaya
yana kallonta cike da mamaki.. hardai suka gama
abubuwansu sukai sallams da mumy suka fita
kasancewar xasu gidansu hameeda anna bikin
yayarta..
suna fita mumy ta kalli Abdul tana fadin "yauwa
dama innason magana Sakai"
Gyada mata kai yayi ta sauna kusa
dashi..kwanciya yayi saman kafarta tasoma fadin
"Abdul nagode Allah da ya shiryamin kai ka dena
shaye shayenan..dab Allah karma kuma ba da
bi'a bace me kyau"
"insha Allah bazan karaba mumy"
mumy taji dadin zancensa dan hk suka fara hira
cike da nishadi...
*Night*
Zaune haneef take ya daga wayarsa ya kira
Abdul bugu biyu ya dauka..
haneef ne ya gayyaci Abdul zuwa gidansu ba
musu Abdul yaje yana zuwa ya iske haneef ya
kofar Gida..motar haneef ya Shiga tare da cema
Abdul suje susha drink...
suna zuwa Abdul yace bayason anytin
alcoholic..murmushin mugunta haneef yayi
yamiqe tsaye tare da fadin
"ok bari ta karboma fanta.'
haneef Na zuwa ya jefa masa wata qwaya
acciki..yana kawo masa ya yazuba masa shiko
beyi tinanin komai ba ya Kaba yasha..cikin Yan
mintina yanayin Abdul ya soma canjawa alamun
ya bugu..
Waya haneef yayi yana fadin "ya guys kusa
akamo mana daya"
can kuwa sukaga wata budurwa dake ta faman
tafiya ita kadai daukarta sukai tana kuka suka
sata a Mora..
(Afreen)
19 hrs · Public
Boost this post for $3 to reach up to 5,700
people.
30 People Reached
[8/7, 3:30 PM] Afreen ce: ~SAFNA TA~
B¥
{Faty afreen}
*👑Queens Online writers*
*(Q.O.W)*👑
_(Home for wisdom & excellent writers)_
*06*
Tana kuka suka sata a mota wani farin qyale
suka sa mata a hanci..jinta kake shiru alamun ta
suma... Dariya sukayi kafin daya daga cikinsu ya
data Waya ya soma yin kira..
Bugu biyu aka saga kiran haneef me saga can ya
Roma fadin..
"Ya dafatan kunyi abinda Na saku?"
"Eh oga komai nrml munsamo wata yarinya.."
Murmushi kawai haneef yayi ya kashe
wayarsa...juyawa yayi ya kalli gadon dake
gefensa..Abdul me kwance shame2..murmushi
haneef Yaya ya soma fadin..
"Abdul innasan kanwarka kaqi bani dama kuma
SBD dukiyarku kadai yasa make tare dakai..kuma
senayi sanadiyar lalacewar rayuwarka..xanyi
farinciki idan naga iyayenka na fishi
dakai..dariyar mugunta haneef yayi Karin ya juya
ya fice da dakin..
*Morning*
Ahankali abdul ya miqe yana Salati tare da safe
kansa..zauniya yayi saga kwanciyar dayake..
Ahankali ya ke bude idanunsa be saukesu kan
komai se yarinyar dake kwance akan gado
..atsora ya ja baya yana Salati.. ahankalivya leqa
danganin wacece..cike da mamaki ya miqe saga
kan gadon ya rarumi kayansa yasa ..dikcya had a
zufa..kofa ya nufa yana buga kofar dakin..
Dams kamar jira ake aka buds kifar cike da
mamaki abdulvya nunavhaneef ganin shi ya shigo
dauke da try na abinci..
*good morning* haneef ya fada..baking abdul Na
rawa ya soma fadin. "Haneef yuh"!!
Yan nunasa da dan yatsa... Murmudhi haneef
yayi yana fadin. "Yeap just wan cheer yuh up
frnd..HP u enjoy yuhr nyyy" be karasa ba seda
abdul ya wankesa da Marin da har sanda try din
hanunsa ya fadi ya akasa..kafin ya karasa fadin
"ttt" din dasauri ya safe kuncinsa idanuwansa dik
sun kada tsabar ya Maru..
"No zakayiwa haka"?acewar abdul.. Haneef kuwa
murmushi yayi tare da tura harshensa ta gefen
kumatunsa inda aka maresa..
Ahankali haneef ya kalli abdul yana fada
"Daga nama gwaninta seka mareni?bakomai Na
yafe maka aikai abokina nane"
Haushine ya kara cika abdul afusace yakai wa
haneef shaqa ya hadeshu da bango..haneef tin
yana dariya taga Cesar abdul dagaske take ransa
ya back dik jijiyar wuyansa da Kansa ta
fitoh..Dan hk haneef ya soma memo ma jansa
dabars tin kan abdul ya kashesa..
Tari haneef ya domayi Hans fadin.. "Kaje jaji da
yarinyar daka sumar wayasanma kota mutu.."
Dasauri abdul ya sake sa tare da kallon inda
yarinyar ke kwance..murmushi haneef yayi ya
karasa gurin da tare hanunsa yasa ze taba
kafafunta..da sauri abdul ya hankada haneef
yana fadin..
"Karka kuskura ka taba min kanwata"
Shiru haneef yayi yana tinanin wace irin kanwa
kuma? Sekuma yayi dariya
"Saga jiya daddare zuwa ysu shine tazama
kanwarka?"
"Naga alamunar taka kanwarce ko?" Abdul ya
fada ransa a bace..
Kara kai hannu hannu yayi ze tabata da Saudi
abdul ya hankadasa karka tabata..kaitamaka
muksi safna asibiti..
Dasauri haneef ya kalli abdul..Dan shikansa
bessn wacece yaran aikin nasa duka dauko ba..
*Asibiti*
Zaune haneef da abdul duke Suns fuskantar
likitan da me mudu magana..magunguna ya basu
Wanda zasu bata kafin suka fitoh..
Wayar Abdul ta soma ruri..dasauri ya dauko
ganin mumy ce yasa gabansa ya fadi yasan
cesar hankalinta nscan a tashe
Ahankali us kara wayarca kunensa..
"Hello abdulrahman inna kashigane? Kaxo banga
safna ba tinjiya bats dawo ba nakirata wayarta
swtch off Kuma nakira hameeda race tin jiya
daddare duka rabu ."
Shiru yayi ya rasa mexecewa mumy dawyarvys
iya furta msta "mumy ganinan zuwa"
Bejira mexata ce ba ya kashe wayar..haneef
dake gefe shima hankalinsa. atashe ya bude baki
zema abdul magana..amma ya kasa sbd harar da
Abdul ya watso masa ..wuceea abdul yayi ya
shigecdakin da safna take..barci takeyi tsayawa
yayi kallonta na yan mintina kafin ya soma
kokarin daukarta ..hannu haneef ya kai tare da
fadin "bari Na taimaka maka"
Ahankali abdul ya kalli haneef tare da fadin..
"Sanda ka cuce ni zakave xaka taimaka min?"
Yans gama fadan hk ya sunkuci safna be tsaya
ko inna da ita ba se cikin motarsa.. Gida ya nufa
da ita sanda ya Shiga kafin yasoma tinanin
mezecewa mumy..intaga safna a inna zece ya
ganta?,,,
Be gama tinaninsa ba ya jiyo sautin muryar
mumy tana fadin
"Abdul kataimaka ka gano min safna"
Daga idon da zeyi yaga harta kusa karasowa inda
yake..nanfa dik ya fibibice yarasacta inna ze
fara..nanma ysga dady ya fitoh fuskarsa shima
cike da damuwa..
Tinani ya somayi akan ys fadamusu gsky?in ya
fada musu kuma bazasuvyafe mass ba Dan
mumy ta hanasa shayeshaye..
(Afreen)
[8/7, 3:38 PM] Afreen ce: ~SAFNA TA~
B¥
{Faty Afreen}
*👑Queens Online writers*
*(Q.O.W)👑*
_(Home for wisdom & excellent writers)_
_I dedicated dis page to all members of *👑Queens Online writers* Innasanku dayawa Allah yabar qauna_
*07-10*
In ya fada musu kuma bazasu yafe masa ba ; Dan mumy ta hanasa shaye shaye...
Dabarace ta fada masa dan hk tin kafin su mumy su karaso ya fitoh daga motar dasauri yana fadin..
"Mumy na gano safna"
Zaro ido mumy da dady sukayi cike da mamaki ganin jikinsu yayi sanyi yasa be karacewa komai ba ya nufi motarsa ya sunkutoh safna wacce har ynxu barci takeyi..be tsaya ko inna ba se cikin dakin mumy ya direta...
Yana cikin gyara mata kwanciya su mumy suka shigo..sautin muryar dady da zancen da yake fada ne yasa jikin abdul yin sanyi..ahankali ya dago zufa na keto masa...
Mumy kuwa bata ni taksnsu ba ta nufi toilet can se gata dauke da bowl din ruwa da karamin towel aciki..
"Abdul a inna kasamu safna?kuma meyasameta?"
Acewar daddy Wanda da ka kallesa kasan yana cikin damuwa..
Hadiyar yawu abdul yayi yana tinanin ta inna ze fara fara ma su mumy bayanin abinda ke faruwa..wata karyar da ze musu yashiga tunanin yi..
"Badakai nake magana ba ka shareni?"
Shiru abdul yayi yana goge gumi daga bisani yasoma fadin ...
"Kayi hkr dady afyade aka ma safna jiya daddare na tsinceta a...*"
Be karasa xancesa ba sbd karar yadda robar ruwan da tayi..
"Mumy meya fa,**
Yakai hannu ze taba mumy dasauri ta dakatar dashi tarr da daga masa hannu..gabansa ne ya fadi jikinsa ya soma rawa..shikansa dady jikinsa yayi sanyi..mumy kuwa miqewa tayi ta nufi daidai saitin fuskar safna tana shafawa se kuma ta fara hawaye..
Abdul na ganin hk yakasa jurewa wucewa yayi ya bar dakin....
Haka mumy da dady sukacigada kula da safna har Allah ya bata lfy..
Yau wata daya kenan mumy nazaune a kan kujera safna ta fitoh daga kitchen dauke da plate din syyan plantain da kwai..guri tasamu tazauna kusa da mumy...
Daidai Abdul zefitoh palo da shirinsa na fita ya jiyo mumy na mgn..Dan hk ya labe Dan jin metakefada..
" ke safna wani irin ciye ciye kike ne hk... Innace dazu kika gama cin indomie"
Turo baki safna tayi tana fadin
"Mumy fa yinwa nakeji"
"Sekiyitayi ai..kiyita ciye2 kamar wata me ciki?"
Zaro ido abdul yayi tare da maimaita abinda mumy tace
"Ciki"😳!!!! Naga takaina..
Fitowa yayi yawa mumy sallama..ta masa addua ya fice yanata kallon safna...
Tafe yake cikin motarsa yana tunanin yanda zeyi inda gaske safna nada ciki yazeyi?
Zancen zuci yafarayi yan fadin
"Gsky in safna tana da ciki dole in aureta SBD baxan bar dana ya sha wahala ba..."
Har ya isa office yana tunanin safna aransa..
Yana shiga ya zauna se yaji an turo kofa..ga mamakinsa se yaga haneef..
Daure fuska abdul yayi ya juya fuska.. Zama haneef yayi akujera..
"Abdul Dan Allah kayi ha"***
Dakatar dashi yayi tare da daga masa hannu..be kara cewa komai ba ya miqe yafice..
Yana fita haneef yayi dariyar mugunta ya jawo karamar wayar abdul daya manta..
Sunan safna yasa..seyaga sunan ya bayyana da ~SAFNA TA~
Tsaki haneef yayi ya kwafe number ya fice abunsa..
*Night*
Dare nayi misalin karfe 9 abdul ya shiga gida kofar dakinsa ya nufa har yakai se kuma ya juyo dakin safna ya nufa ahankali ya tura kofar dakin...
Beganta a dakinba Dan hk ya juya xe fita ga mamaki se yajiyota a toilet tana amai..
Kasa karasawa yayi jiki asanyaye ya bar dakin ya nufi dakinsa...yana shiga ya fada kan gado yashiga tunanin iri iri..har barci ya daukesa...
Safna kuwa tana fitowa ta tarar da misd cal har biyar..tsaki tayi ta ajiye tana zama akan gado wayarta tasoma ruri..ahankali tadauka ta kara a kunenta...
*" Assallam masoyita dafatan kina cikin koshin lafiya"* zaro ido tayi cike da mamakin wa****.....😁
(Afreen)
[8/7, 3:47 PM] Afreen ce: ~SAFNA TA~
B¥
{Faty Afreen}
*👑Queens Online writers*
*(Q.O.W)👑*
_(Home for wisdom & excellent writers)_
Dedicated dis page to
Swt darling
*💖Abba gana💖*
(Allah ya kara ma lafiya da daukaka..ya kareka daga Sharrin maqiya)
✍✍✍
*11-15*
*"Assallam masoyiyata dafatan kina cikin koshin lafiya"*
Zaro Ido safna tayi cike da mamakin wanene wanan?bude baki tayi da niyar magana amma ya cigaba da fadin
"Nasan zakiyi mamakin wayeni.kuma nasan kina cike da tambayoyi..na baki dama zaki iya mun su"
Shiru safna tayi tadanyi murmushi kafin tayi ajiyar zuciya tana fadin
"Hmm sannu da surutu zan iya sanin dawa nake magana?"
Tana gama fadan hk tayi murmushi bayan ajiyar zuciyar da yayi hade da murmushi..
"Kiyi hkr bangabatar miki da kaina ba daga farko...nakama kunnena ayafemin ko sena tsuguna?"
Murmushi safna tayi me sauti kafin ta ce "baka fadamin abinda na tmbyk ba"
"Hmm..Sunana jameelu ahmad amma Anna kirana da haneef..kuma inna aiki a NNPC..ynxu hk inna garin Kaduna naje aiki but jibi zan shigo kano insha Allah"
"Hmm toh sannu haneef..nagode da kira?". " toh baki fadamin naki sunan ba".
Murmushi tayi kafin ta cigaba da fadin "Bakasanni ba zaka kirani?"
"Ayi hkr afadamin sunan ko sena siyane?afadomin tsadar sunan"
Wata iriyar dariya safna tayi kafin ta tabe baki daga bisani ta cigaba da fadin
"Sunana safna"
""Woooow Safna!!!!!! Yafada in low voice.."
"Gsky nayi sa'a..zan iya kiranki da safna ta?"
Dariya tayi sosai ta jawo pilo ta rufe fuskarta kamar tana kallonta..waya sukayi sosai kafin sukai sallama.....
Safna bata kwanata ba sanda ta miqe ta nufi kitchen dan nemo abinda zataci...abdul na kallon fitar ta daga daki..shima yabi bayanta Dan ganin me zatayi..
.
Itako tana shiga kitchen ta bude flask din dake dauke da jellof din shinkafa. Toshe hancinta tayi da Saudi tare da rufe Kular da Sauri..
Sake baki abdul yayi yana kallon ikon Allah kamar ba dazu ta gama ci ba
Tsaki yayi yabar gurin ya koma dakinsa.....
Tindaga ranar kusan kullun safna smda haneef se sunyi waya...abdul kuwa ba abinda baya siyowa safna sedai in beji ta fada cewar tana so ba..kuma inya siyo baya bata sedai yashiga dakinta ya ajiye yafitoh abunsa...
Lokacin da mumy suka gane safna nada ciki kwatakwata basu soba amma ba yadda zasuyi da qaddara dole suyi hkr..
Safna kuwa tasha kuka kamar ranta zefita har zazzabi ta dingayi abdul kuwa dik inda hankalinsa yake ba akwance bane muddin yaji ance safna bata da lfy..tin mumy na hakuri har wataran ta kirasa dakinta...
"Abdul meke damunka ne?narasa ganema dik kabi karame ka lallace. Da wanne zanji?da rashin lafiyar safna ko da halin dakajefa kanka..kodai shaye shaye ka komai?"
Arikice abdul yadago ya riqe hanun mumy
. "wlhi mumy bana shaye2 nadena wlhi..kwai mumy tausayawa safna nakeyi tanashan wahala"
Yazamuyi abdul dole muyi hkr addu'a zamudinga mata Allah ya sauketa lfy..
.
Ameen suka fada a tare ya kwanta akan kafar mumy itako tana shafamasa kansa. ..
Safna ko har haneef ta basa labarin tanada ciki a halin ynxu...ransa ya baci amma be nuna mata..shiko ya qudiri niyar seya auri safna ya tozarta abdul
Akwana tashi ba wuya shikin safna ynxu wata 8...nanfa abdul yakara daukan so ya dorawa safna .amma ynxu yaqi yarda da Sonta yake...acewarsa akan abinda take dauke dashi ne kwai...
Kayan wasa iri2 abdul yadinga siya yana ajiyewa babu Wanda yasani..dakinsa kuwa kullewa yayi ko mumy ya hanata shiga dakin..
Ranar da safna tahaihu ba ayi taro ba amma sanda abdul ya yanka mata rago..shi ya dage akan zesa ma yar suna..
Ga mamaki yasama yar sunan mumy inda safna ta samata miemie...da abdul ya fara fitowa da kaya kuwa kowa sake baki yayi yana kallonsa sbd mamaki...
*back to current*
Kwance safna take tana waya ..miemie nata faman kuka..
Safna kuwa ko ajikinta kasancewar tasan ba kowa agidan dik sunfita har mumy..
Da haneef taketa waya tana murmushi abinta..
"Wai jinjirarki ce taketa kuka hk?" Acewar haneef daga can
"Mtsw!! Tsaki safna tayi tana fadin qyaleta tayi tayi ko ajikina wlhi kokadan banajin san yarinyarnan a zuciyata"
Shiko haneef daga can murmushi yayi tsabar dadi..kanyayi magana cigaba da fadin
"Dan Allah yi hkr bari na fita a dakinan ta da meni da qara"
Amsaa mata yayi da toh daidai ta miqe zata fita kenan..taji an hankado qofa..
Abdul ne ya shigo a fusace idanunsa sunyi ja sun kada...tana kaninsa ta sake wayar akasa ta haye kangado tana ihu tana ba sa hkr........🤓
(Afreen)
[8/7, 3:50 PM] Afreen ce: ~SAFNA TA~
By
{Faty Afreen}
*👑Queens Online writers*
*(Q.O.W)👑*
_(Home for wisdom & excellent writers)_
Dedicated dis page to
*Afreen Novel's Series*
*16-20*
Kusa da ita ya nufa dad da ita ya tsaya har suna shaqar nunfashin juna...
Cikin rada ya fara mata mgn
"Safna y?? Meye damuwarki meyasa kike haka?"
Yana kaiwa nan ya miqe ya sunkuci miemie suka fice daga dakin..
Ajiyar zuciya ta sauke ta fada kan gado tana maida nunfashi wayarta ta hango Wanda se aynxu kiran haneef ya qatse dasauri ta miqe tadau wayar ta ma haneef flash
Ba bata lokaci ya biyo kiranta..hkr ta basa suka cigaba da hirarsu..
*Gidan anty amina*
Anty amina kanwar dady ce tanada yara hudu..biyu maza biyu mata..Hafsah da hanan sai kabir da kamal..
Dik agidansu dady tafisu kirki kuma sunfi shirin da abdulrahman dik wata damuwa tasa yakan kai mata akai akai..
Haka yauma tinda yadauki miemie gidan ya wuce da ita..
Yanazuwa su hanan na murna suka karbi miemie..
Hafsah wacce ke zaune tana ganin abdul ta miqe tashige daki dan itako son abdul take sosai acewarta kunyarsa takeji amma shiko bemasan ta nayi ba..
Palo suka zauna shida anty amina Wanda suke kiranta da mami..
Zama tayi akan kujera ya zauna kusa da ita ya kwantar da kansa saman kafarta...
"Abdul meyafaru ne? Daganinka akwai magana"
Gyada mata kai yayi alamun "eh"
"Toh fadamin in naji meke faruwa"
Kafin yayi magana hafsah ta shigo dauke da try plate din abinci ne da kuma ruwa ta ajiye agabansa tare da gaidasa ya amsa..se wata karairaya takeyi amma Sam shi hankalinsa baya gareta..
Hartakai qofa taji ya fara magana Dan haka ta labe Dan jin make faruwa..
Mami yau zan fada miki sirrin Dana Dade inna boyewa nakasa jurewa mami saboda nasan banma safna adalci ba😪
"safna kuma !!shine abinda hafsah ta fada tare da yamutse fuska adai iya saninta ya abdul basa shirin da safna.. Acewarta ma tana mamaki ya akai haryake daukar miemie qila Dan yanda son yarane kuma basu da yara"
Muryar mami ce ta dawo da ita daga tunanin data fada
"My son ka kwantar da hankalinka ka nutsu ka fadamun meke faruwa?"
"mami banason mum da dad suji in sukaji zasuyi fushi dani sosai kuma balaifina bane"
Hafsah na jin haka tayi saurin kunna wayarta tasa a voice recording... Qara matsawa ciki tayi dan jin meze fada sosai..
"Mami safna"!! Na mata laifi nasan bazata taba yafemin ba"
"Yishiru kaji kanutsu kafadan meke faruwane?"
Nanfa Abdul ya kwashe kaf labarin abinda yafaru taba mami..mami ta cika da mamaki zancen ta..
Hafsah kuwa kasa tsaya wa tayi agun tayi save din Wanda ta record ta shige daki tana kuka sosai..
"Ynxu miemie yar' kace?"
Mami ta fada cike da mamaki..
Gyada kai abdul yayi yana share hawayen fuskarsa..
Kayi shiru shiyasa son tinfarko banga meyakaika fara shayeshaye ba abokai mugayene inba mutun yasamu nagari ba ahalin ynxu sesu cutar da mutun gashi kai ynxu yacutar dakai..
"Mami kitaimakamin na auri safna innasanta in nasan miemie"
Shiru mami tayi kafin daga bisani ta soma fadin
"Bakomai tashi kaje abinda zan samu mahaifin naka insha Allah komai zedaidaita.."
"Amma mami kimin alkawarin bazaki fada musu nine mahaifin miemie ba"
"Akan me abdul?"
"Insuka sani ynxu zasu hanani ita. Bayan anyi auren se inmusu bayani ko?"..
" shknan abdul Allah ya maka albarka ya qara shirya mana kai...yakuma rayata"
"Amin ya fada Dan yaji dadin addu'ar mami..abincin yasomaci badan yana masa dadi abaki ba sedan yinwar da yakeji"
Hafsah kuma tana fadawa kan gado taci kukanta me isarta kafin ta miqe zaune
idanunta sunkada sunyi jawur..
Miqewa tayi ta zauna kafin ta kunna recoding din da tayi ..
Murmushin mugunta tayi da gefen bakinta..
"Wannan Abun shi ze zama makami agareni dole ya abdul ya aureni kuma dole ya soni"
Wani murmushi ta kumayi kafin ta kashe ta miqe..
*Washe gari*
Abdul ne ya shawo kwana daidai ya zo baking gate kenan ya hango safna da haneef suna tsaye..
Kasa dauke idansa yayi daga garesu..
"Haneef da safna!!! Me hakan ke nufi?"..
Haneef na ganin sa sukayi ido hudu ..Jan motar abdul yayi tashige ko parking be gyaraba ya shiga ciki mum ya gani tana rirriga miemie dake barci..
" abdul ya akayi meyafaru "?
" mum meyasa safna zata fita gurin wancan bazan?"
"Yau naga ikon Allah inna ruwanka ka qyaleta mana ..tinda yasamu Wanda takeso baashikenan ba"
Qara fusata abdul yayi piiii yawuce yashige dakinsa jikake Biuuum ya bango qofar..
Wayar dady ce ta soma ruri anty amina ce yadauka cike da fara a..
Suka gaisa kafin ya tmbyt meke faruwa bata sanar dashi komai ba illa tanason magana dashi..
Cewa yayi xesameta agidanta inyadawo daga aiki..
Amsa wa tayi da toh kafin sukayi sallama.
(Afreen)
No comments:
Post a Comment