[9/7, 6:20 PM] Real Afreen ceπ: π‘π‘π‘π‘
π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
~Rikicin~
*{Babban gida}*
Na
_Faty Afreen_
_Bismillahir rahmanir rahim_
_Agsky banda bakin da zan yi muku godiya masoyana kun nunamin qauna kun sani farinciki sosai kun qaunaci wannan littafi nawa..da writers din da readers dikka inna godiya ba a dadi agareku_
Wannan shafi nasadaukar dashi gareku members din group din *Rikicin babban gida fans* nagode daaddu'ar Ku
Kuma wannan shafin tukwici ne gareku
*Fadeela lamido*
*Sadieey smart*
*Action baby*
*Hassan basiru Yusuf mafia*
*Halimatu YB hassan*
*Slim small*
*Didi lurff*
Nagode sosaiππ
Vote me on watpadd
@Fatyafreen1
_Book 2π_
Episode *1-5*
Misalin karfe 9:30 ta fitoh daga dakinta daidai ta fitoh sukayi cinkaro da ammy
"Ahhh amra yaushe kika shigo bansani ba"
"Bandade ba ammy nazo duba abune gibe zanzo saida safe ammy"
Sallama sukayi ta fice daga part din
Cikin sallamarta ta shiga part dinsu Arman ganin ba kowa a palon yasata nufi dakin safiya kwance ta isketa tayi sallama ta amsa mata..
Cire hijab din tayi ta kwanta kangado
"Amra mekikama ya arman? Ko baki fada masa kin fita bane"
Cikin sauri amra ta dafeqirji
"Meya faru?"
"Yazo nan nemanki ransa da alama abace ne kije kiji meyasa yake nemanki"
Jiki sanyaye amra ta shiga toilet ta watso ruwa kayan barcin ta tasanya kafin ta dau hijab dinta zata fita safeena ta kirata..
"Ke kixo ki feffesha turaruka mana"
"Wai dalili"
Amra ta fada tana yaysine fuska..
"Inkika dauke masa hankali cikin soyyy zakufi warware matsalarku.."
"Nikam barni naje naga kiran me yakemin"
"Kedai dama akwai ki da kafiya"
Harar Safeena amra tayi kafin ta fice.
Jikinta na rawa ta shiga dakin zaune ta samesa ya jingina da jikin bango akan gado sallama tayi har so biyu be amsa ta ba idonsa na rufe..
Gaba daya tausayinsa ya kamata ta hawaye kawai takeyi kusa dashi ta matso ta zauna jikin gadon hanunsa ta kamo ya fizge..
"Ya Arman kayi hkr wallahi inna sonka"
Sai ynxu ya bude idonsa da yayi jawur ya kalleta kafin ya qara rufewa batare da yace mata komai ba
Fuskarsa amra ta riqe da hanuwanta wuyansa ta taba taji jikinsa zafi xau...
"Ya arman zazzabine ya jikinka meyasa meka..bara na kawo ma abinci da magani"
Bedai ce mata komai ba ya miqe ta nufi kitchen indomie ta dafo masa da kawai ta hado masa tea tare da maganin zazzabi Dana ciwon kai ta kawo masa..
Table ta jawo kusa da gadon ta dora abincin dik tabi ta rude..
"Ya arman dan Allah kaci ko na baka ne abaki"
Bude ido yayi ya kalleta tare da gyara zaman sa yana fuskantar abincin
"Yauwa ya arman dan**"
Bata kaiga qarasa zancen ta ba ta zubar da dikka plates din akasa suka farfashe har tea din ya zuba mata akafa ihu tayi agigice tana kuka tana kiran sunan mum..
Cikin hanzari mum da safiya suka shigo daidai nan Daddy yashigo palon yajiyo hayaniya dakin arman din ya nufa..
"Arman yazaka zuba mata tea mezafi haka a qafa idan ka qonata fa"
"Mum wayace tazo kusa dani..banason ganinta"
Cikin sauri amra ta kalli ya Arman.. Saitaqara fashewa da kuka..
"Meke faruwane?"
Acewar dady
"Yauwa gwara da kazo ka gani da idonka yaronan tinda ya dawo baya ragawa wannan baiwar Allah nan mumy ta kwashe komai ta fadawa dady cikin bacin rai"
"Arman dama kasan bakasonta dan ka muzguna mata kasa aka dawo da ita nan din?toh kayi gaggawar sauwaqe mata ta huta"
"Daddy nifa bazan saki mamata na"
Mum ce cike da takaici tasoma fadin
"Kasan matar takace kake mata wannan Abun haba Arman gsky baka kyautawa"
Daga Amra mum tayi wacce jikinta tayi sanyi dan dik ta zata ya arman sakinta zeyi..dakin safeena suka nufa safeena na biye dasu abayanta...
Dady ransa baceya fice yana fadin
"Zanyi ma ganinka"
Zama arman yayi saman gado yafara kuka yana tuno hotunan da kuma riqewar da hydar ya mata...
*2weeks*
Tinda safe Safiya ta shirya ta fice ta nufin gidansu qawarta maryam nan su kasha hira kafin suka tafi wajan wani malami..
"Mallan dama"
"Nasan meyaa kawoku akan saurayine da kkso ko?"
Yana nuna safiya..gyada kai safiya tayi tana kallon maryam da mamaki ..
"Mesunan saurayin"
"Arman sunansa yanada mata"
"Eh dik nasani.."
Rubuce rubucensa yayi a saman qasar dakegabansa yana surutansa daga bisani yasa hannu kusa dashi yadauko wata baqar Leda ya miqa ma safiya kallon maryam tayi ta gyada mata kai kafin safiya ta karba hanunta na rawa..
"Wannan kisiyo lemo Wanda yafi so kisa masa shi aciki idan kuma babu ko acikin cake irinsu kayan ciye ciyenan ki bar bada masa ki basa yaci amma se yayi kwana biyu kafin magani ya fara aiki..."
Murmushi safiya tayi na jindadi sosai kafin ta ta ce
"Malan nawa xa'abaka"
"Dubu goma"
Zaro ido safiya tayi maryam ce tayi caraf tana fadin
"Haba mallan mudai bada dubu biyar ai gaba se muji dadin dawowa"
Wata irin dariya mugunta yayi kafin yace kukawo bakomai...
Hannu safiyatasa cikin jaka ta Ciro kudi ta qirga ta basa yako karba kafin suka miqe suka fice..
*Night*
Kwance Arman yake amra ta kuma shigowa dakin da sallama ya amsa kallo daya ya mata ya dauke kansa yau ta masa kyau sosai tafi kullun ma amma ya maze ya juya abinsa
"Meyasa kakizo min daki"
"Ya Arman nagaji da irin xaman da mukeyi ykmt mu tsaya mu fahimci juna idan ma laifi nama ka na baka hkr"
"Banason mgn dake amra..bakya sona nariga nasani mezesa in tsaya sauraronki..kinmin karya za kije gun ammy kin tafi yawon gabanki"
Gaban amra ne ya fadi qoqarin magn tafarayi se ta fara qaqarin yin amai dagowa yayi ya kalleta fuska a hade yana fadin
"Ke kuma meye hk?"
"Bako***"
Bata qarasa ba ta qara wani qoqarin aman tare da to she baki
Kallonta yaqara yi yana fadin
"Lanki kuwa?"
"Eh laaaa***"
Wani qaqarin anan tafarayi tayi saurin to she bakinta
Tsaki yayi Abun ma dariya yafara basa
"Meye kuma hk sabon salon mene hk"
"Wallahi ya Ar****"
Wani qaqarin anan ta soma yi yaqara toshe bakinta
Besan sadda dariya ta kufce masa ba
"Wallah baki da***""
Beqarasa zancensa ba tayi wataqara da gudu ta ada toilet dina ta fara kwara amai kamar ranta ze fita kamar wani soko ya taso yana leqenta...
Mum ce taturo qofar tana fadin
"Arman Kaine ke amai hk"
Tsaye taganshi yana nuna mata toilet din leqawa tayi taga amra..
Murmushi tayi ta shiga toilet din..
"Mehakan ke nufi"
Afada bemasan yafitoh fili
Kamar daga sama yaji mum tace
"Abinda kake tunani shi aman ke nufi"
_Toh fans me kuke tunani wanda aman ke nufi?_
*Real Afreen ceπ*
[9/9, 6:53 AM] Real Afreen ceπ: π‘π‘π‘π‘
π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
~Rikicin~
*{Babban gida}*
Na
_Faty Afreen_
Dedicated to
*My nemcy Maman shaheedπππ*
_Godiya nake gareku fans kun so novel dina sosai..inna kaunarku ako yaushe_
Book 2π
Sunan wanga episode *Fire on d mountain*π₯π₯
Episode *6-10*
Kamar daga sama yaji mum tace
"Abinda kake tunani shi aman ke nufi"
Shiru Arman yayi ya kasa ko rufe bakinsa..sanda ta gama aman tukunna mum tariqota suka fitoh
Bin amra kawai yakeyi da kallo yarasa ma mezece sai murmushi yakeyi..
"Sannu amra"
Acewar mum
Amsawa Amra tayi kafin ta tana dafe da cikinta da qirjinta
"Ko kina bukatar wani abu?"
Acewar Arman
Cike da mamaki dik suka dago suka kallesa bama kamar Amra
Gyada kai tayi alamun a'a
Yayi murmushi sai mum tace
"Toh ynxu dai tashi kitafi ki kwanta gobe dasafe sai kuje asibiti"
Beso Amra ta tafi ba amma kuma nauyin mum yakeji sosai yarasa ta innazefara mata mgnr abar masa matarsa annan
Riqe ta mum tayi suka nufi kofa itama bataso tafiya ba dan so take ta basa hk waiwayansa takeyi seya daga hannu ze mata alamartazo sai mum tajuyo se yafara Sosa qeya
Mum na ankare zasu amma setayi kamar batasan sunayi badik da dai mamaki na cikata sosai yaza ayi ace Amra Nada ciki iya saninta tinda Arman yadawo basa jituwa...
Dakin safiya Amra ta shige tarasa yadda zatayi mumce tashigo tana fadin
"Amra ki kwanta ki huta kinji ko kina bukatar wani abu"
A'ah mum acewar amra..mum sanda ta tabbatar amra ta kwanta kafin ta shige dakinta
Can ko Arman ya kasa sukuni so yake yama amra mgn ya tabbatar abinda mum take nufi gsky ne..
Dabara ce tafado masa cikin sauri ya zaro wayarsa ya soma kiran wayar safeena bugu biyu ta dauka
"Hello yaya"
"Sister inna amra plxx kice tazo innajiranta"
Cike da mamaki safeena ta juya tana kallon Amra wacce keta faman murmushi ita kadai mamaki abin ya bata
"Kije ya Arman na nemanki"
Kamar dama jira take tayi wuf ta mike zata fita cikin sauri safeena ta ruqota
"Haba matar yaya gsky zoki canja shigarki kidansa turare"
"Ke wai meye haka"
"Ke wallahi sekinyi wanka ma zaki fita"
"Cikin mamaki Amra tace toh bazanyi ba"
Miqewa safeena tayi ta kulle qofar tana fadin
"Seki zaba kokije kiyi wankan kokuma kifasa fitar"
Ba yadda Amra ta iya dole ta juya ta shige toilet ba jimawa ta fitoh Cikin murmushi safeena ta miqe ta bata turaruka ta fesa itadai amra batace da ita komai ba aranta tana fadin
"Indai yayankine zakigama kiyi asarar turarukanki a banza a ohfi"
Amra ko tafiya tayi gurin sip dintadauko nightist dinta Riga da wando ta sa kafin ta kalli safeena tana fadin
"Zaki samu damar bani key din"
Wurgo mata tayi tana fadin
"Ayi barci medadi karki dawo min dakina"
Tsaki kawai Amra tayi ta fice abunta..tana zuwa qofar dakin Arman ahankali ta murda ta shiga ga mamakinta sai ganin shi tayi tsaye ita yake kallo..
"Ya Arman plxxx ka tsaya ka***"
"Shiiiiiii ya isa babyna am so sory"
Kuka tafashe dashi taje ta rungumesa tana fadin
"Wallahi a hotonan shi ya shigo inna barci kuma ranar naje masa mgn akan hoton ne"
Qara rungumeta yayi tsam daga bisani ya zaunar da ita shima yana share hawayen afuskarsa
"Toh baby laifinkine da tin lkcin da Abun ya faru baki fadamin ba and ranar kikamin qarya"
Cikin rawar jiki hanuwanta na rawa ta ruqo fuskarsa
"Ya Arman am sory plxx kayi hakuri"
Zama yayi kusa da ita yasata a qirjinsa yabshiga rarrashinta...
Bayan wasu mintina sai yasoma fadin
"Baby meyasameki fadamin inji"
"Dasauri tana murmushi ta daga fuskarta tana share hawaye gwanin ban tausayi ta ruqo hanunsa tana fadin
"Ya arman babyn mu ne..taba kaji"
Kamar wani soka ya duqe kasa tare da sa kunensa kan cikin ita kuma ta riqe kansa yana fadin
"Hyyy little angel its yuhr days..dftn kn lfy..just say hy to me"
Dariya sosai Amra takeyi ya Arman ya dago yana fadin
"Baby yaqimin magana.."
Dariya tayi kafin tace
"Nima bamemin ba ai"
Dariya sukayi ya rungumota jikinsa nanfa salon ya canja kashe wutar dakin yayi nikuma nayii waje abuna...
*Washe gari*
Da asbah Arman ya tashi ya tashe Amra sukayi wanka kafin ya jasu sallah..
Suna idarwa yasa hannu saman cikinta yana fadin
"Ya little angel din mu"
"Murmushi tayi tana fadin tace ingaisheka"
Cikin sauri ya dagata ya dora ta kan gadon ta zauna kafin yasa kunensa akan cikin nata yafara yan surutansa
"Ya Arman bara na tafi kar mum ta fitoh innan"
Riqeta yayi gam yana fadin
"Haba babyna inna zaki plxx karki tafi"
"Kayi hkr zan dawo"
Bayadda ya iya dole ya saketa ta fice daga dakin...
Gari na wayewa safeena ta hada brk yaukam Amra na barci bata samu tayata ba dan hk safeena ta mata uziri...
Tana gama wa suka fitoh suna brk amma ba amra leqe kawai yakeyi yaga ta inda zata fitoh tashi shiru mum na ankare dashi dan hk tashe
"Safeena inna amra ne"
"Barci takeyi" safeena ta bata amsa
"Jeki tadota in her condition ynxu ykmt tasamu abu taci"
Dasauri Arman ya miqe
"Mum bara na dubota"
Bejira cewar mum ba yayi gama dik sai suka rakasa da ido....
Yana shiga ya isketa tana shafa mai ajikinta Allan ta fitoh daga wanka jingina yayi da qofa ya nade hannu yana kallonta..
Jitayi shirun yayi yawa a tunanin ta safeena ce ta shigo dan hk ta juya kawai se ganin Arman yayi dasauri ta soma qoqarin sa hijab dinta dake gefe
Cikin sauri ya qarasa ta riqota jikinsa
"Mezaki boyemin baby ko kunyata kikeji"
Rungometa yayi a jikinsa sosai suka kwanta shaff ya shagala da mum tayi aika a kirata..
Canko mum abinduniya ya isheta be ykmt ace tin Amman jiya ba har ynxu amra bata ci komai ba..
Miqewa mum tayi ta ta nufi hanyar dakin ahankali ta murda kofar dakin tana fadin
"Arman aikan Dana maka kenan"
Cike da kunya dik suka miqe girgiza kai kawai Mum tayi ta fitoh ta baro su..
Amra ko sip dinta ta nufi doguwar Riga ta dauko tasa ta juya yazage mata zip din sanda ta gama komai kafin suka fice..
Brk suka zauna yi seyaga kamar ba a kallon su seya sama amra baki junansu suke kallo sunata murmushi..bude baki yayi akan tasa masa daidai takai bakinsa kenan mum ta juyo tana fadin
"Yauwa idan kum**"
Mamakine ya kamata ganin abinda sukeyi ko kunyar zaman ta agun basuji ba..dan hk tamiqe tare da karasa mgnr ta
"Idan ka gama kuje asibiti adubata"..
Toh ya ansa dashi tana wucewa ya raka safeena da kallo dolenta ta tashi tabbasu guri amra ko ta rakata da gwalo..
Nan sukasha syyrsu..
Amma suna gama vin abinci nan amra ta nufi toilet kaf kayan cikinta sanda ta Amayar dashi...
Tambayarta yashigayi mezataci amma tace dashi ba komai ... Jiki sanyaye ya dauketa suka nufi asibiti...
*Real Afreen ceπ*
[9/9, 2:17 PM] Real Afreen ceπ: π‘π‘π‘π‘
π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
~Rikicin~
*{Babban gida}*
Na
_Faty Afreen_
Dedicate dis page to
*Anty Zarah bukar*
Sunan wanga Episode *Fire on d mountain*π₯π₯
Book 2π
Episode *11-15*
Tambayarta yashagayi mezataci amma tace dashi ba komai.. Jiki sanyaye ya dauketa suka nufi asibiti
Gwaji aka mata Wanda hkn ya tabbatar musu da cewar Amra na dauke da juna biyu..
Wani irin dadi Arman ya qara ki sosai kamar ya goya amra har kyautar dan dalasimai(kudiπ) yama likita kafin suka taho gida...
Kansu kawo gida ta fara barci amota suna zuwa ya sunkuceta safiya na kallonsu takaici ya cikata dakinsa yakaita yana fitoh mum ta tmbysa harsun dawo eh kawai yace ya miqa mata zaka makon ya fice yanata murna...
Tana budewa ta tabbatar da hasashenta kuma taga alamar cikin na Arman ne tinda murna yakeyi be daga hankalinsa ba..daga hanuwa mum tayi sama tare dayin addua akan Allah ya sauki Amra lfy ya kara hada Kansu..
Dady na zuwa mum tasanar mishi shiko Arman dakin goggo ya nufa nan yake bata lbr ai amra nada ciki..
Murna sosai goggo takeyi kan kace me dik iyayenan sun San halin da ake ciki anata sa alheri harda masu musu kyauta ma..
Anty Amarya kotanajin zancen ta kira hydar akan yazo yasameta ba bata lokaci ya zo
"Wat!!! Umma ciki kuma dikka dikka yaushe yadawo?"
Acewar hydar
"Nima abinda yakeban mamaki kenan kuma ni aganina anya cikin dake jikinta na farko ya zube kuwa?"
"Kumafa hakane umma amma nasan abinda zanyi"
"Yauwa son kayi dik abinda ya kamata"
Ficewa yayi daga dakin daidai Arman ya fitoh kenan sukayi cinkaro da sauri hydar ya taresa
"Yauwa dama kai nake nema kayi gaggawar bani Amra SBD cikin nan nawane ba naka ba"
"Kai kana da kankali kuwa?"
"Kaine baka da hankali ka kacemin mata ynxu kuma harda Dana"
Arman ne yafusata da kalaman hydar dan hk yakaimasa duka..
Fada ne ya kaure a tsakaninsu Arman harya fara jima hydar ciwo SBD baza a hada qarfin hydar da Arman ba..
Anty Amarya ce ta fita tana ihu
"Wayyoh na shiga uku ze kashemin Dana"
Kanka ce me dik an fiffitoh mum ma hk Amra dake barci itama ta taso tare sa safeena suka fita Safiya ma da su goggo da Ammy dik sun fitoh
"Meke faruwa ne?"
"Kawai daga na fadi gsky shine ze kama dukana"
Acewar hydar
Amra ce tazo ta riqe ya Arman tana basa hakuri
"Wallahi hydar zanma abinda baka tunanin"
"Toh qarya anyi?amra tawa ce kuma cikin jikinsa nawane dama be zube ba kuka min mugunta"
Kowa mamakin furucin hydar yayi
"Kaii hydar amma baka da hankali ko?"
Acewar goggo
"Goggo kadena cemin bani da hankali Arman ne bashidashi"
Saukar mari kawai hydar yaji Abban sa ne dan hk ya nutsu
"Goggo kake fadawa haka?cikin da yake jikin Amra dikka watanshi nawa toh Wallahi zanma abinda baka tunani"
Anty Amarya ce ta soma fadin
"Haba Abban hydar toh wallahi da na hydar ne kuma a haifeshi a basa abinda ehen"
Tana kaiwa nan taba hydar suka shige part dinsu kuwa ya sake baki ya bisu da kallo...
Amra ko zubewa tayi qasa sumammiya bashiri kowa yayi kanta...
*Hours ago*
Farfadowa amra tayi taga Arman kusa da ita yana riqe da hanunta..
"Ya Arman"
Dasauri ya dago yana kallonta fuskarta FAM da fara'a
"Baby sannu"
Kuka kawai ta farayi tana fadin
"Ya Arman karka bari su kwace mana baby"
"Shhiii karki damu babyna ba Wanda ya isa"
Rungumeta yayi mum ta shigo dauke da abinci ..ya Arman fita yayi domin yin sallah ya barsu agurin...
Bayan yayi sallah ne ya dawo ya nufi part din goggo ya jiyo safiya na anbaton sunansa..
Juyawa yayi yana murmushi
"Ahh safiya kece"
"Eh ya Arman ga cake dazun na hada na ajiye maka innata cigiyarka se ynxu naganka"
Miqamasa cake din tayi aleda ya karba yana godiya
"Bara na gaida goggo"
Toh tace masa ya juya abinda kallonsa kawai take tana murmushi
"Kayi hkr ya Arman nasan matarka da danku dake cikinta suna bukatarka amma kuma nafi bukatar ka sosai..kaci lafiya zaka zama nawa"
. dariya tayi tana juyawa tayi cinkaro da hydar..
"Ohhh ya hydar Kaine"
Tafada tana qoqarin daure fuskarta...
"Mekike shirinyi?karki kuskura haukanki ya taba Amra idan ba hk ba zaki raina kanki"
Turo baki tayi tana fadin
"Ni ba abinda zanyi ka kyaleni"
.
"Nidai na fadamiki ki kiyayeni"
Yana kaiwa nan ya juya ya tafi ya barta tsaki tayi itama ta shige part dinsu abinta...
*Night*
Kwance amra take kusa da ya Arman suna hira
"Nidai khadija za a samata"
"Tabb banyarda ba ya Arman sunan mum za a sa mata"
"Cab toh in ansa mata fatymah me za adinga cemata?"
"Afra"
Wow sunan mum dinta da dad dinta daga A itama hk...
Dariya suka dingayi suna fado sunaye...
Asbah nayi Arman yayi alwala ya tashi Amra kafin ya fice zuwa masallaci yana fita tabiyo bayansa dan ta ce masa kan yadawo zata shiga garin Ammy..
Fita tayi tana duba sa amma bata gansa...
Morning
Gari ya waye sosai Arman ya shigo yana dubawa ko inna beganta ba ..safeena ya kiraamma tace bata ganta ba gun goggo ya nufa batanan
Har part dinsu ya shiga ya tmbyi qanenta amma dik su kace basu ganta ba...
Rikicewa yayi ya yashiga Neman Amra amma beganta ba...
Ita ko goggo shigar Arman Ashe ya manto cake din sa yana shiga ta basa yace ta ajiye masa...
Ganin beganta ba har kusan karfe 12 yasa ya koma part dinsu still beganta ba kwadawa mum kira ya farayi
"Mum!mum! Kizo Wallahi banga Amra ba"
Fitowa mum tayi arikice
"Kaiii son me kake nufi ka nutsu mana"
Ya bude baki ze qara mgn yaji wayarsa na ruri da sauri ya dauka
"Hhhhh Arman kenan matar taka da kake nema tana gurin mu"
Wani qato ya fada daga can..
Kukan Amra ya sa masa tana ihu sai suka kashe wayar
Kiran layin ya dingayi amma akulle..
"Mum sun dauke min matata mena musu" zubewa yayi qasa yana kuka mum ta ruqosa tana fadin su waye?
Azabure ya miqe yana fadin mum nasan hydar ne hydar ne..afusace ya fita mum tabi bayansa tana kiransa...
*Real Afreen ceπ*
[9/9, 4:05 PM] Real Afreen ceπ: π‘π‘π‘π‘
π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
~Rikicin~
*{Babban gida}*
Na
_faty Afreen_
Dedicate dis page to
*All ma fans*
Vote me on watpadd as
*Fatyafreen1*
Book 2π
Episode *16-20*
Azabure ya miqe yana fadin mum nasan hydar ne ! hydar ne!!..Afusace ya fita mum tabi bayansa tana kiransa..
"Son ka tsaya karkayi zarginsa baka tabbatar ba"
Arman ko yana fita tsakar gida yafara kwadawa hydar kira...ba'afi yan mintina ba Hydar ya fitoh
"Ya akayi ne kkson kararmin da su***"
Beqarasa zancen sa ba Arman yakai masa duka abaki har sanda yaji masa ciwo Abaki
"Mena maka yau kuma zaka dakeni haka?"
"Inna matata take?ka fitoh min da mata"
Qoqarin riqeshi mum takeyi amma inna yaqi..
Fitowa akayi Anna basa hkr amma dukan hydar yake..
"Inna matata take"
"Ribar mezanci na dauke Amra ko zan dauke wani kai zan dauke ni banma ga amra ba"
Dady ne yaso da sauri ya dauke Arman da mari
"Bakada hankali ne kaje ka nemi matarka amma ka tsaya dukansa yace maka beganta ba"
Hydar ne ya juya ya kalli dady yana fadin
"Wallahi dady bansan inda Amra take ba nibanganta ba"
Anty Amarya dake gefe tasoma fadin
"Nashiga uku indai jikana nakeji"
Takaici taba yan gurin gaba daya Ammy ko tun tana jurewa ta fashe da kuka tana fadin
"Dan Allah kunemomin Amra ya zanyi dan Allah kutaimakamin"
Riqeta mum tayi ta shiga rarrashinta tariqeta suka shiga ciki Arman ko juyawa yayi yaje yadauko key din motarsa ya yadau motar ya fice...
Hydar dake qaaa ya miqe shima yana qoqarin fita
"Inna zakaje" acewar anty Amarya
"Umma Amra zan gano"
Tabe baki tayi ya juya...safiya dake tsaye tana kallon dik abinda ke faruwa tayi saurin bin bayan ya hydar tana fadin
"Ya hydar tsaya dan Allah"
Tsaya wa yayi yana kallonta ta qaraso ta na murmushin mugunta
"Ya hydar kenan ko kowa ze yarda da cewar bakai ka daki Amra ba to ni bazanyarda ba"
Tsawa yayi yana kallonta da mamaki
"Ke safiya me kike nufi ?"
"Hhahaha Nasan ka fuskanci inda na dosa kadena wani wayincemin kawai in kana Neman taimako kakirani SBD nasan kaika dauketa..innasan ya Arman kanason Amra kowa seya daki Wanda yakeso.."
Dariya ta qarayi ta wuce abunta tana fe tana waigensa shiko sake baki yayi ya tsaya yana kallonta...
"Toh meyasa kowa yakezargin shi ya dauki amra?"
Tabe baki yayi ya bude qofa ya fice..
Arman dake cikin Mota dik inda ya tsaya seya nuna hoton Amra ..hydar ma haka yake tayi..
Gab da magrib hydar ya dawo dik aka masa caaa amma yace musu ba bayani...
Kuka kawai suke tayi kowanensu na tausayawa Amra...
Mum ko tama Arman kira yafi aqirga amma bedauka ba..
Goma saura yadawo gida dik ya jigata ya fita daga hayyacinsa...
Mum na zaune bakin qofa taji horn dinsa kamar akan kunen ammy ta fitoh tana tmby amma shiru kaf gidanan kowa ya rikice daqyar mum ta kama Arman takaisa dakinsa...
Kuka kawai yake yi sosai yana tuna amra..
Tuno ranar da ta dinga qaqalo amanan yakeyi yana kuka da hirarsu akan sunan da zasu sama babynsu...
Da yadda ya bata abinci abaki ranar da safe itama ta basa da lokacin da yakesa kunensa a cikinta suyita dariya...
Kuka yaqara fashewa dashi ya rasa inda zesa kansa kamar mahaukaci yayi sauri ya kawo wayarsa yasoma kiran number dinan ga mamakinsa number ta shiga...
"Hhhhh tindazu muke jiran kiranka baka kiraba"
"Dan Allah mekukeso agurin kome kikeso Ku fadamin xan Baku kubani matata"
"Hhaaahhhhaaa ba abinda muke buqata sai abinda ke cikinta"
"Subhannallah dan Allah kutaima kamin dan Allah"
"Hhhhh karka damu xamu kula da ita har ta haihu kafin mu dauki abinda ta Haifa mudawo maka da matarka"
Ihun Amra ya jiyo tana kuka tana kiran sunan sa...
"Dan Allah kuyi hkr kudawomin da matata"
"Hhhhh ba wannan zancen mallan mun baka minti biyar ka yi mgn da matarka"
Samata wayar akunne akayi tana kuka shima kukan yakeyi
"Babyna kiyi hakuri dan Allah"
"Ya Arman plxxx kazo dan Allah"
"Zanzo baby I prmx I will help yuh out.. Kinci abinci"
Tana kuka ta amsa da eh tare da tmbyrsa shifa a a yace mata nanfa fara roqonsa akan yaci abincin fizge wayar sukayi suka tashe wayar kuka tasa musu tana ihu
Wani daga cikinsune mesona bobi ya miqe ya fadin
"Ke kinga damemu da ihu ko kiyi shiru kona bindigeki ynxu"
Shiru kawai tayi tana hawaye zaune take saman kujera sun daure mata qafafuwanta sa hannuwanta acikin kujerar...
Kasan cewar nan taje wuni dare anyi zasu shige da ita wani dani da akwai katifa aciki susata su kulleta aciki..
Arman ko daqyar yake tura abincin badan yana jindadinsa ba...
*Washe gari*
Yan samarin gidanan da magidantan kowa ya kama gabansa kowanensu na baza tasa basirar iya qoqarin sa dan anemo amra amma Abun shiru...
Hydar ne ya gama shirinsa ya fitoh motarsa ya hau ya fice daga gidan yana fita safiya tabi bayansa har inda yaje
Wani uncompleted building ne gidan daidai nan ya tsaya ita ko tun daga can hanya tasauka daga napep ta qaraso da qafa..
Kwakwasawa yayi yashiga inda aka daure amra ne barci takeyi ya tsaya yana kallonta yana murmushi...
Tafi suka faraji meyi na shigowa ciki ga mamakinsa sai yaga safiya..
"Haba ya hydar dama nacema baxaka taba rainamin hankali ba"
Shaqotayi yayi waje da ita suka fitoh daga gurin
"Kasakeni me zaka boyemin bayan nariga na gani"
*Real Afreen ceπ*
[9/10, 6:47 AM] Real Afreen ceπ: π‘π‘π‘π‘
π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
~Rikicin~
*{Babban gida}*
Na
_Faty Afreen_
Godiya nake ga masoyana nagode sosai qaunaku nake sosai yan uwanaπππ
Book 2π
Episode *21-25*
Shaqota yayi yayi waje da ita suka fitoh daga gurin
"Kasakeni me zaka boyemin bayan nariga na gani"
"Meyasa kika biyoni inna ruwan ki dani"
"Ka sakeni Wallahi ko kayi aikin dani ko kuma in tona ma asiri"
Dafe kansa yayi yayi tsaki tare da buga bango
"Mtsw shknan naji abinda zakimin shine kidinga samun ido akan take taken Arman"
Fari tayi da idanu tana fadin
"Angama ynxu dai matsamin inje infants dan shine farin cikina"
Dariya tafarayi yayi saurin toshe mata baki kamar me amra tayi firgigit ta tashi da sauri hydar yaja Safiya suka labe abaya allamu yama yaransa su shige da ita cikin dakin
Bamusu suka aikata hakan..Hydar ne ya qara shaqo safiya yana fadin
"Meyasa wai baki da hankaline"
"Indai banda hankali toh kaima bakada kaji min fa"
"Mtsw dallah rufamin baki ki wuce mu tafi"
Tsaki tayi tayi gaba tana fadin
"Dik boyanka wataran seta ganka kawai mallan inzaka bayyana mata kanka kabayyana ehe"
Hartakai gaban motar tasa yana binta da kallo..kafin ya juya yafara bawa yaransa kudi akan dik abinda tace tana bukata su siya mata...kafin shima ya nufi motarsa...
Suna son isa gida Arman suka gani a zaune yayi jugum ya Tisa wayarsa agaba yana kallo ganin su yasa ya bisu da idoshi dai yasan basa shiri toh me yasa suke tare ynxu?..
Itako ganin yana kallonta yasa Tayi murmushi aranta tana fadin kodai ya Arman yafara sontane shiyasa yake kallonta haka..
Shikuma miqewa yayi yashiga ciki dan bayason ta damesa da surutu
Tana ganin tashige tayi dariya tana fadin
"Lallai ya Arman yafara sonta kishinta yakeyi dan ya ganta da hydar .
Dariya ta kumayi tana fadin
" bazan kulaka ba har seka kawo kanka tayi dariya kafin ta nufi part dinsu"
*Washe gari*
Zazzabi ne jikin ya Arman sosai mum ta rasa yadda zatayi wuni yakeyi yana gwada number n amma ko wanne lokaci akulle..
Yana cikin wannan tunanin ne da bara ta fado masa akan ya tafi wajan masu system can cmm.centre ya tsaya da akankira da numbern se amsa tracing agano inda suke..
Wanka yayi daqyar mum tasashi yaci abinci ya nufi part din ammy ya gaidata dik ya rame yazama wani iri dashi..
Part din goggo ya nufa yana zuwa yagaidata kafin ya miqe ze fice
"Yauwa Arman ga ajiyarka"
"Wacce ajiya goggo?"
"Cake din daka kawo aleda"
"Cab aiko na manta dashi be lallace b?"
Dauko cake din tayi tamiqa masa ya bude ga mamakinsu cake din be lallace ba
"Toh goggo ki cimana"
"A'a jeka da kayanka dazanci da tuni naci"
Murmushi yayi ya rufe ledar ya fice da ita...
Daidai ya bude motarsa kenan ya ajiye cake din ya zauna yajiyo muryar safiya na kiran sunansa cikin sauri yasa hanki dinsa dake gefe ya rufe cake din dan banaso taga beci ba..
Ita ko sauri take ta qaraso taji inda zashi dan kar ya bata musu wasa daya fada mata saita sanar da hydar...
"Safiya ya"
"Lfylau ya Arman inna zuwa haka?
Murmushi yadan qaqalo kafin yasoma tunanin ko dai ya fadama ta ne saima ya tafi da ita ta taimaka masa in case in sun gano inda amra take?
Murmushi yaqara yi yana fadin
*Real Afreen ceπ*
[9/11, 2:07 PM] Real Afreen ceπ: π‘π‘π‘π‘
π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
~Rikicin~
*{Babban gidanan}*
Na
_Faty Afreen_
_Saqon gaisuwata ga masoya littafina *Rikicin Babban gidanan* kuma nagode da adduar da kuke min Inna tare daku_
Book 2π
Episode *26-30*
Murmushi yaqara yi yana fadin
"Haba safiya wacce iriyar tmby ce wannan Neman matata zani mana"
"Toh bara naje na tayaka"
"Safiya ki barshi kawai nagode"
Yana fadan hk ya yada motarsa yayi gaba abinsa...
Shiru ta tsaya tana tunanin kodai beci cake din bane kam can kuma seta tuno mallan yace mata ai yana daukar kwanaki tabe baki tayi tashige ciki domin kiran hydar...
Abban amra ko ya gama rikicewa police station ya nufa ya sanar dasu tare da bada hotunan amra ammy ko rashin lafiya yakamata sosai...
Arman ko inda yaje hk ya wuni agurin basu kira ba yaki ra amma akulle har wajan karfe 10 sanda suka zo kullewa kafin ya tattaro kafafuwansa yadawo gidan...
Zaune ya iske mum a Palo gurinta yaje ya zauna a kasa tare da kwantar da kansa kan kafarta kuka yakeyi sosai
"Mum ynxu ta inna zan fara neman amra bansan ya akayi ba"
Daqyar mum ta rarrashesa ta basa abinci yaci...
*washe gari*
Wajan karfe 9 Arman yagama shiryawa ya fitoh domin qara komawa wajanan najiya kallo daya za ama Arman asan yana cikin damuwa gaba daya yarame mgn ma ta kirki gagararsa takeyi...
Daidai ya fitoh kenan yaga Abban amra tare da police gurinsu ya qarasa tare da gaidasu dikka sosai Abban amra ya tausayawa Arman idanuwansa dik sun kumbura kamar bashi ba...
"Abba anji wani labarine akan ta?"
"A'a Arman sunce sunaso su fara bincike daga nan cikin gida..tinda Kaine mijinta ykmt kamusu bayanin karshen ganinka da ita".
Safiyace ta leqo ganin police a gidan yasa ta rikice ta dibibi ce bashiri ta koma ciki ta shige dakinta
Wayar hydar tafara kira Wanda yake can wajan da ya ajiye amra
" hello safiya yane"
"Wayyoh mun shiga uku su ya Arman sun kawo yan sanda acikin gida"
"Mtsw ke fa banxa ce ki zauna a dakin ki kar kifita kije ki tona mana asiri..inna zuwa ynxu"..
Toh kawai tace suka katse wayar ba abinda jikinsa yakeyi banda rawa leqe tadingayi ta window..can ko arman ya fara musu naegani
" Nidai ranar daddare ta kwana a gida saboda a dakina ta kwana ma ranar kuma har asbah na tasheta tayi sallah kafin na fita shknan Dana dawo na nemeta na rasa"
"Toh anan ba Wanda kuke zargin ze iya aikata hakan?ko bawanda ta taba fada dashi?"
Arman ne yayayi saurin fadin
"Nidai inna zargin hydar Abba dan Allah kasasu su tintibe hydar ynxu xanje ni gurin danaje jiya ko Allah zesa su kira"
Toh Abba ya amsa tare da masa fatan samun sa'a..hydar aka shiga nema amma aka tabbatar baya nan anty Amarya ko sai masifa take akan anma yaronta sharri...
Safiya ko qara kiran hydar tayi akan karya dawo gida nemansa ake..
Toh ya amsa dashi tare da Neman mafita...
Dabarace ta fadawo Hydar yakira daya daga cikin yaransa Wanda yakesawa yana kiran Arman tafada masa abubuwan da ze fadawa Arman idan ya kirasa...
Isar Arman gurin kenan ba da dadewa ba wannan mutumi ya kira...aiko Arman ya amsa yan gurin suka fara aikin su na tracing din inda suke...
"Arman bakajin mgn ko bakason lafiyar matarka ko?"
"Innaso mana wacce irin mgn ce wannan dan Allah Ku dawo min da matata"
"Inna sane da cewar kunsa yansanda wajan ne manta toh ka gaggauta cire yansanda a zance nan idan ba hk ba sedai kaga gawar matarsa"
"Hakuri Arman ya fara basu"
"Mun baka 2hrs ka kauda zancen yansanda a wannan lamarin"
Basu jira jin mezece ba suka kashe wayar..
Murmushi Hydar yayi ga mamakinsa se yajiyo muryar safiya yashigo gurin cikin sauri ya qarasa
"Ke ya akayi kika fitoh"
"Kai tsoro nakeji bazan iya zama a gidan ba"
Tsaki Hydar yayi ya juya abunsa gun da amra take suka nufa..
Hydar ya tsugunna aganta fuskarta dikta kumbura saboda kuka..
"Tststs babyna ji yanda fuskarki ta kumbura'
kamar amafarki taji muryar hydar tana bude ido taga hydar gefensa safiya kuka tafashe dashi
" menayi muku me nayi muku zaku dinga min irin hk"
Kiciniya ta shiga yi hydar yayi dariya ya miqe yana fadin
"ke kika bijiremin yayinda nikuma nake qaunarki"
Dariya yayi kafin suka fice shida safiya daketa hararta..kuka amra tadinga yi tana ihu...
Arman ko can sunriga sunyi tracing din gurin da suke fada masa wurin sukayi ya musu godiya tare da biyansu kudi har fiye da Wanda suka tmby..
Barack din sojoji dake garin ya nufa tare da musu bayani yanuna musu id card dinsa sukagane shisojane yanada 2rang
Anguwar yamusu kwatance da ya umarce su da karfe 3 su zo gurin..
Tafiya yayi ya kama hanyar gurin sukuma su safiya sun baro gurin da nufin zuwa gida...
*Real Afreen ceπ*
[9/11, 4:15 PM] Real Afreen ceπ: π‘π‘π‘π‘
π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
~Rikicin~
*{Babban gida}*
Na
_Faty Afreen_
*Dik Wanda ya jefeni da Kalmar nan bemin adalci ba..banda girman kai kuma banga mene abin yi aciki ba*
_plxxx kar Wanda yasa min book 2 dinan a document har sena gama zansa dakaina me buqata yamin mgn banajin qyashin turowa amma kar asamin a doc. Plxx_
Vote me on watpadd as
*Fatyafreen1*
Afreennovelseries.blogspot.com
Like my page on Facebook
*Afreen novel's series*
Join my group on Facebook
*Faty Afreen novels*
Book 2π
Episode *31-35*
Tafiya yayi ya kama hanyar gurin sukuma su safiya sun bark gurin da nufin zuwa gida....
Tafe yake yana shatata gudu amotarsa ba abinda yakeyi banda gumi..wayar ya qara kira yaji akulle..
Busar da iska yayi ya cigaba da tafiya yana tafe yana addua..
Tafe yake har ya isa gurin suko su safiya da hydar har sun bar gurin..yana zuwa ya paka motarsa can da nisa ya fitoh ya nufo gurin da gidan yake...
Can ko su safiya suna isa tindaga bakin gate safiya ta sauka ta qarasa da qafarta shiko ya shiga da motarsa gabansa ne yafadi ganin harynxu yansandan na nan suna zaune...
Yana fitowa Abban amra ya kirasa yagaidasu kujera yasa yazauna
"Abba Allah dai yasa naga amra?"
"A'a amma dai tambayoyi za a maka ne"
Zaro ido yafarayi yana fadin
Toh toh toh innaji
Dan sandan ne yafara tambayarsa..safiya ko takasa qarasa part dinsu tana labe jikinta na rawa
"Yaushe rabonka da Amra kafin batanta"
Kallon abba yayi kafin yasoma fadin
"Gsky yakai kwana biyu zuwa uku"
********
Can ko Arman cikin labe yake leqensu suna zaune tacan gefe..
Amra dake ciki Ashe tin zuwansu Arman kick kicin data farayi saurin da suka mata ya kunce..
Jin motsinsu shiru yasa ta miqe ta dauko wayar da suke kiran Arman dashi dake ajiye can gefe ...
Arman ko cikin taku ahankali ya isa bayann gidan yana qoqarin shiga kenan wayarsa ta soma ringing kamar daga sama Amra tajiyo ringing din wayarsa...
Qoqarin fitowa tayi taga daya daga cikinsu yataso dik se suka taso gaba dayansu labewa tayi..
Arman da ya samu ya kashe wayarsa yana laben yadda zeyi ya shiga gidan be ankare ba se ji yayi an kwadesa akai..
Faduwa yayi qasa yatare da dafe kansa yana fadin subhannallah...
Daya daga cikin sune yazo da gudu yana fadin
"Oga yarinyar fa tagudu"
"Wat!!!!"
Marin dayan yayi yana fadin
"yuh are very stupid jeku nemota"
Arman dake zaune kansa na sarawa ya soma kiran wayar hydar...
Hydar dake zaune annata masa tambayoyi dik ya hada zufa miqewa yayi yayi gefe kamar muna fiki yana ansa wayar yana waiwayonsu..
"Hello ya akayi"
"Oga wani gaye yazo nanfa kuma yarinyar ta gudu"
Tsaki Hydar yayi Aransa yana fadin Allah yasa ba Arman bane..
Qin komawa gun yan sanda yayi ya nufi motarsa suna kallonsa ya shige motarsa yana shiga safiya ta lallaba ta shiga gidan baya..
"Ya hydar inna zaka".
Arazane ya juyo yana fadin wayyoh Allah dan dik yagama tsorata ganin safiya yasa yayi tsaki..
" wani yaje gurin kuma inna zargin Arman ne"
"Cab bazani ba sauka zanyi"
"Aiko baki isa ba Wanda yasa kishiga motar"
Ke yasama motar tasa tana ta roqonsa amma inna yaja motar...
Yansandan dake zaune gurin ne suka miqe sukawa Abba sallama batare da yasan hydar zasubi ba..
Qin hawa motarsu sukayi suka tari taxi suka dinga binsa abaya..
Canko Arman tattaro qarfin sa yayi yardage yana qafar wannan qataon ya zube aqasa ji kake timmmm
Daukar ican yayi shima ya rafka masa akai da qafarsa...
Ihu kawai wannan qaton keyi... Amra dake labe tana nunfarfashi icce tagani abayan ta dasauri ta dauka suko cansun bazama neman ta..
Wani tagani ya shigo yana shigowa ta dage ta rafka masa aka ya zube qasa sanda ya fadi tukun ta lura Ashe Arman ne
*Real Afreen ceπ*
[9/11, 5:55 PM] Real Afreen ceπ: π‘π‘π‘π‘
π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
~Rikicin~
*{Babban gida}*
Na
_Faty Afreen_
Dedicated dis page to all members of
*Afreen novels series*
Vote me on watpadd as
*Fatyafreen1*
Book 2π
Episode *36-40*
Wani tagani ya shigo yana shigowa ta dage ta rafka masa aka ya zube qasa sanda ya fadi tukun ta lura Ashe Arman ne...
Hannu tasa ta rufe bakinta ta tsugunna tana hawaye ya Arman ka tashi nice..
Ahankali ya dago ya kalleta sekuma yakoma ya kwanta SBD irin ciwon da kansa yake masa...
Jin motsinsu suna mgn ta soma tada sa
"Ya Arman ka tashi karsu xo"
Se motsi kawai yakeyi canko sunanta mgn da Alamar hydar da safiya sun iso
"Inna suke?"
Acewar Hydar
"Wallahi Oga bamu gansu ba"
Tsaki safiya tayi tana fadin
"Ku banzaye ne dallah kujeku nemosu"
Kowa kama hanyar gabansa yayi...
Hydar ya kalli safiya yana fadin
"Zo muduba ciki bazamu bari su tona ma asiri ba"
Jin hydar ya fadi hk yasa Amra taja da bayata dinga Jan Arman har sanda suka shige inda ta boye...
Sandar ta qaradauka ta riqe Arman daya miqe zaune ya tsaya kallonta tana sharar hawaye ta riqe cikin nata
Miqewa yayi yarungumota ta baya harta tsorata ya toshe mata baki yana fadin
"Shiii baby nine"
Fashewa tayi da kuka ta rufe bakinta tana ajiyar zuciya ya rungumota jikinsa yana lumshe ido
Daidai nan su hydar suka shigo ya kalli safiya yana fadin
"Kiduba can bara na dubanan"
Cire jikinta tayi daga nasa ganin safiya gurin da mamaki yaga safiya iccan ta kwadawa safiya safiya ihu safiya tayi ta zube qasa
Ihun Safiya ne ya dawo da hankalin Hydar ya juya ya nufi gurin yana zuwa yaga safiya zube akasa..kalle kalle ya farayi yaji antabasa yana juyawa Arman yakai masa naushi Arman be ankare ba yaran Hydar suka rirrikesa..
Dariya sosai hydar yakeyi...
"Inna kike ki fitoh konasa akashesa ynxu"
Cikin rawar jiki Amra ta fitoh tunani Arman yafarayi me ya hana sojojin zuwa ne...
Daga hannu hydar yayi zekaima Arman duka yaji bindiga akansa diksesuka bi gun dakallo yana juyawa yaga wannan police din daya baro...
Qarar motar sojoji sukafara ji da sauri yaran suka sake Arman suna Neman guduwa...
Suna dirawa tawindow sojojin dake gun sukayi ram dasu...
Dukan qafar hydar akayi ya zubeaqasa police mace dake gefe ce ta daga safiya tayi wajan da ita hydar ma haka...
Kuka Amratasa dagudu ta nufi gurin Arman tana kuka
Rungumeta yayi ajikinsa suka nufi waje suna zuwa sukaga Abban Amra dadady tsaye awaje da gudu Amra taje tarungume Abban ta
Police din ya kalli Abba yana fadin
"Dama kunsan nan ne?"
Murmushi Abba yayi yana fadin
"A'a ganin hydar yafl fita kuma kun fita yasa nacema dadyn Arman mubi bayanku kawai"
Shigewa sukayi Mota dikkansu..su hydar kuwa policesl station aka sample dasu.
"Da Allah Arman ka yafema dan uwanka hydar dan Allah kar abata zumunci wlhi baze qara ba"
Arman beko kallesu ba yasoma fadin
"Amra zaku tmby tafiya ai"
Nanfa aka dinga basu hakuri akan suyafe daqyar suka hkr amma sedai su hydar da safiya suyi 2mth ko 3 a prison...
Tindaga ranar Arman yadauki matarsa yayi tafiyarsa da ita gun aikin sa
*End*
_A duniyar nan mu kasance muna masu biyayya Amra tin farko datayi biyayya bata kai kanta ga hydar ba da dik hkn bata faru ba dik da Ance kaddara ba makawa_
Allah yasa mudace
Godiyata
*Rikicin babban gida fans*
*Afreen novels series*
*Fadeela lamido novels*
*Baiwa Associations*
*004.Hausa novels*
And odas
*Gaisuwata gareku*
*Asy Khaleel*
*Mum Shaheed*
*Anty wasila*
*Sadieey smart*
*Fadeela lamido*
*Slim small*
*Didi lurff*
*Pretty queen*
*Ayusha ilias*
*Zarah bukar*
*fido yar ficika*
*Action baby*
*Mum Nawal*
*Cwtjiddah*
*Khairyyy*
*Hassan Basiru Yusuf magia*
*Halimahtu yb hassan*
And oll odas
~Alhamdulillah~
*Real Afreen ceπ*
No comments:
Post a Comment